Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci miliyan biyu ne mazauna birnin Moscow na kasar Rasha, suka bukaci da a kara yawan masallatan birnin bisa la’akari da karancinsu,inda ya zuwa yanzu manyan masallatai hudu ne kawai ke akwai a cikin Moscow, wanda muslmin suke ganin cewa ko alama wannan adadi bai wadatar ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo CNB an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci miliyan biyu ne mazauna birnin Moscow na kasar Rasha, suka bukaci da a kara yawan masallatan birnin bisa la’akari da karancinsu,inda ya zuwa yanzu manyan masallatai hudu ne kawai ke akwai a cikin Moscow, wanda muslmin suke ganin cewa ko alama wannan adadi bai wadatar ba, tare da yin kira da a duba korafin nasu.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani bangare guda kuma a cikin wani byani da ya fitar bababn sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi, ya bayyana irin wadannan ayyuka na ta'addanci da gwamnatin yahudawan sahyuniyan take aikatawa kan fararen hula palastinawa da cewa aiki ne da ya yi hannaun riga da dukaknin ka'idoji da kuma dokoki na kasa da kasa, a akn ya kirayi dukkanin gwamnatoci masu fada a ji da suke safke nauyin da ya rataya kansu.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Nuakshaut fadar mulkin kasar Mauritaniya tare da halartar masana da kuma makaranta gami da mahardata na kasar ta Mauritania. 777648