IQNA

Taron Duniyar Musulmi Da Warware Matsalolinsu A birnin Makka Mai Alfarma

13:08 - April 21, 2011
Lambar Labari: 2109542
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken taron duniya da kuma duniyar musulmi,tare da tattauna muhimman hanyoyin warware matsalolinsu, wanda babban kwamitin shirya tarukan addinin musulunci na birnin zai dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Makka mai lafarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafion sadarwa na yanar gizo na SPA cewa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken taron duniya da kuma duniyar musulmi,tare da tattauna muhimman hanyoyin warware matsalolinsu, wanda babban kwamitin shirya tarukan addinin musulunci na birnin zai dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Makka mai lafarma da ke cikin kasa mai tsarki.
Wani labarin kuma ya yi nuni da cewa babbar kungiyar malaman addini na jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta fitar da wani bayani da ke yin kakkausar suka kan keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wasu la’anannu suka yi a kasar Amurka da suna ‘yancin fadar albarkacin baki, da hakan ya hada hakoron tunzura mabiya wasu addinai kan addinin musulunci da mabiyansa.
An gudanar da zanga-zanga da dubban daruruwan mutane suka shiga a cikin kasashen musulmi daban-daban domin yin allawadai da dukkanin wadanda suke d ahannu wajen aikata wannan mummnan aiki, wanda ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinai na duniya.
Al'ummomin musulmi daga sassa daban-daban na duniya suna ci gaba da nuna fushinsu dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansu malaman kiristanci suka yi a cikin kasar Amurka a cikin wannan mako.
777614

captcha