Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa; komitin da ke kula da harkokin addini a kasar ta malaishiya MAIWP Sun ware wani kasafin kudi na musamman day a tashi miliyan dari da hamsi na Ringit domin gina masallatai da makarantun addini a wannan kasa.Wannan mataki na gina makarantun islama da kuma masallatai a wannan kjasa da ked a yawan musulmi zai taimaka matuka gaya wajan inganta al'adun musulmi da kuma uwa uba bangaren ilimi da koyarwa irin ta addini a wannan kasa ta Malaishiya.
777534