IQNA

Rusa Masallatai Babbar Keta Alfarmar Ababe Masu Tsaki Ne A Musulunci

15:07 - April 24, 2011
Lambar Labari: 2111107
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addnin muslunci a kasar Bahrain Ayatollah Isa Ahmad Kasim ya bayyana cewa, rusa masallatai mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya suke yi a acikin kasar Bahrain babban cin zarafi ne da ketar alfarmar addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labarai da ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar rasid an bayyana cewa, babban malamin addnin muslunci a kasar Bahrain Ayatollah Isa Ahmad Kasim ya bayyana cewa, rusa masallatai mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya suke yi a acikin kasar Bahrain babban cin zarafi ne da keta alfarmar addinin muslunci, shehin malamain ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar hudubar juma’a abirnin Manama.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain Nabil Rajab ya bayyana cewa, gidan sarautar kasar ta Bahrain na kokarin tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, da nufin kawar da hankulan al’ummomin duniya kan barnar da suke tafkawa a cikin kasar, suna yin hakan ne kuwa ta hanyar rusa masallatai da wuraren tarukan addini na mabiya mazhabar iyaln gidan manzon Allah masu rinjaye a kasar.
Daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Bahrain Abdulkarin Abduljalil ya bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu bore a fadin kasar.
779091



captcha