Bangaren siyasa da zamantakewa; taron mai taken musulunci da kuma yaduwarsa a tsakanin kasashen duniya da mu'assisar yin nazarin musulunci ta kasa da kasa a Malaishiya ta shirya a ranar bakwai ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya daga misalign karfe tara da rabi agogon kasar zuwa karfe sha daya da rabi tare da hadin guiwar cibiyar Galdom Wab.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa'; taron mai taken musulunci da kuma yaduwarsa a tsakanin kasashen duniya da mu'assisar yin nazarin musulunci ta kasa da kasa a Malaishiya ta shirya a ranar bakwai ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya daga misalign karfe tara da rabi agogon kasar zuwa karfe sha daya da rabi tare da hadin guiwar cibiyar Galdom Wab.Akwai kungiyoyi da hukumomi na ciki da wajan kasar ta Malaishiya da kuma na kasa da kasa da kuma masana da kwararru da malamai da za su halarci wannan taro da a cikin zauren za su yin nazari da bincike kan hanyoyin inganta lamarin.
778895