IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani Kan Mu’ujizar Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Jorrdan

15:04 - April 26, 2011
Lambar Labari: 2112502
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar kur’ani mai tsarki da kuma adabi a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin ilimi da adabin musulunci ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra’y an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar kur’ani mai tsarki da kuma adabi a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin ilimi da adabin musulunci ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin na Aman.
A wani rahoton kuma an bayyana cewa a wani labari da aka nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na middle East Monitor cewa, ana shirin bude hanyoyin karkashin kasa da yahudawan sahyuniya suka gina karkashin masallacin Qods mai alfarma, a lokacin da al’ummomin duniya gami da shugabannin larabawa suka yi gum da bakinsu kan wannan tabargaza ta yahudawan sahyuniya a wurare masu tsarki na al’ummar musulmi.
Tun bayan da yahudawan sahyuniya suka fara gudanr da wannan aiki, masu ‘yancin siyasa daga cikin kasashen musulmi da kuma ‘yan kadan daga cikin kasashen larabawa, sun nuna rashin amincewarsu da wannan mummanan aiki da ke samun cikakken goyon baya daga gwamnatocin Amurka da munafukan larabawa, musamman ma wadanda suke da dangantaka ta zahiri da haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma masu dangantaka ta bayan fage.
780611


captcha