Bangaren kasa da kasa, shugaban masallacin birnin paris fadar mulkin kasar Faransa Dalil Bubakar ya bukaci da a dage gudanar da zaben shugaban kwamitin musulmin kasar Faransa zuwa wani lokaci nan gaba, saboda rashin samun daidaito tsakanin musulmin yankunan kasar, da suke da hakkin zabar wanda suke ganin ya dace.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari dabari da yanaklto daga shafin sadarwa na yanar gizo nalejdd an bayyana cewa, shugaban masallacin birnin paris fadar mulkin kasar Faransa Dalil Bubakar ya bukaci da a dage gudanar da zaben shugaban kwamitin musulmin kasar Faransa zuwa wani lokaci nan gaba, saboda rashin samun daidaito tsakanin musulmin yankunan kasar, da suke da hakkin zabar wanda suke ganin ya dace da rike wannan babbar amana.
Ya ci gaba da cewa wasu yankunan kasar faransa suna da musulmi da dama, wasu kuma akwai karancin musulmia acikinsu, saboda haka ya kamata har wadanda suke da karancin musulmin a basu damar shiga cikin wannan zabe, ta yadda hakkin wani ba zai saraya ba, wanda kuma hakan na bukatr karin lokaci kafin hada sunayen dukkanin musulmin yankuna.
Shugaban masallacin birnin paris fadar mulkin kasar Faransa Dalil Bubakar ya bukaci da a dage gudanar da zaben shugaban kwamitin musulmin kasar Faransa zuwa wani lokaci nan gaba ne, saboda rashin samun daidaito tsakanin musulmin yankunan kasar, da kuma yin adalci a wurin zaben kmar yadda ya kamata.
780576