IQNA

Za A Fitar Da Kur’ani Mai Tarjama A Cikin Harshen Bangala A Yanar Gizo

16:10 - April 26, 2011
Lambar Labari: 2112567
Bangaren kasa da kasa, pira ministan kasar Bangaladash ya bayyanacewa nan ba da jimawa ba za afitar kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin Bangala a cikin shafukan yanar gizo, wanda zai taimaka ma masu bukatar sanin tarjamar kur’ani da suke fahimtar wannan yare.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na The Daily Star an bayyana cewa sheikh Husainiyeh pira ministan kasar Bangaladash ya bayyanacewa nan ba da jimawa ba za afitar kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin Bangala a cikin shafukan yanar gizo, wanda zai taimaka ma masu bukatar sanin tarjamar kur’ani da suke fahimtar wannan yare na asia.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nasij kuma an bayyana cewa, za aguudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar ilimin kur’ani mia tsarki da kuma sunnar manzon Allah (SAW) wanda za agudanar a karo na goma a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar masana daga sassa na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro an sabar gudanar da shi a kasar ta Turkiya, wanda ma’aikatar kula da ayyukan addinin musuluci ta kasar ta kan dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kowace shekara, tun daga shekara ta dubu biyu da daya da ta gabata, inda masana kan gabatar da laccoci da kuma makalolin da suka tanada kan hakan.
780292



captcha