Bangaren kasa da kasa; za a kaddamar da talbijin ta hanyar Internet ta mmusulmi a cikin harshen faransanci mai suna Muslimedia.tv kuma za a kaddamar da ita ne a daidai lokacin fara azumin watan Ramada mai daraja na wannan shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da biyu hijira kamariya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; za a kaddamar da talbijin ta hanyar Internet ta mmusulmi a cikin harshen faransanci mai suna Muslimedia.tv kuma za a kaddamar da ita ne a daidai lokacin fara azumin watan Ramada mai daraja na wannan shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da biyu hijira kamariya.Wannan gidan talbijin na Internet zai rika watsa shirye-shiryensa cikin harshen faransanci da kuma zai kaddamar da shirye-shirye masu kayatarwa domin bawa musulmi masu Magana da harshen faransaci damar samin sanayya kan addininin musulunci da musulmi a fadin duniya.
781037