IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan iraniyanci da Farisanci A Sudan

Bangaren nazari da ilimi: an kawo karshen taron karawa juna sani kan halayyar iraniyawa da kuma harshen farisanci a karo na biyar a kasar Sudan da ke nahiyar Afrika.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an kawo karshen taron karawa juna sani kan halayyar iraniyawa da kuma harshen farisanci a karo na biyar a kasar Sudan da ke nahiyar Afrika. A lokacin gudanar da wannan taron karawa juna sani kan halayyar Iraniya a tarihi da zamantakewarsu da kuma shi kansa harshen farisanci an samu halartar yan jami'a da suka nuna gamsuwarsu da wannan taro da kuma yadda suka gamsu da bahasin da malamai dam asana a dakin taron suka gabatar.

781437