Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar ilimi ta hauza abirnin Karbala mai alfarma za ta gudanar da wani babban gangamin yin Allawadai da mahukuntan kasar Bahrain kan keta alfarmar ababe masu tsarki da suke yi a kasar da sunan murkushe masu zanga-zangar lumana a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sautul iraq cewa, babbar cibiyar ilimi ta hauza abirnin Karbala mai alfarma za ta gudanar da wani babban gangamin yin Allawadai da mahukuntan kasar Bahrain kan keta alfarmar ababe masu tsarki da suke yi a kasar da sunan murkushe masu zanga-zangar lumana.
Bayanin ya ci da cewa a kasarin mutanen da suka rusa masallatai wadanda suke cikin jami'an tsar one ko kuma suke samun kariya daga jami'an tsaron, bayan da mahukunta suka ba su umurnin su yi hakan, kuma da dama daga cikinsu ba mutanen asali ba ne na kasar Bahrain, kuma bayan sanar da sunayensu duniya za ta gani, tare da hotunansu a lokacin da suke tafka wannan ta'asa.
Za a fitar da sunayen dukkanin wadanda suke da hannu kai tsaye wajen rusa masallatai da wuraren ibada da kuma kone kur'ani mai tsarki a kasar Bahrain, bisa la'akari da musun da mahukuntan kasar suka yi dangane da wadanda aka ambata cewa suna da hannu wajen rusa masallatai a kasar.
781352