IQNA

An Nuna Wasu Kwafin Kur'ani A Baje Kolin Littafai Na Kasa Da Kasa A Chille

13:21 - April 30, 2011
Lambar Labari: 2113995
Bnagaren kasa da kasa, an nuna wasu kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harsunan faransanci da Spaniyanci a babban baje kolin littafai na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Sandiago na kasar Chille, wanda ya kara kayatar da wannan baje koli.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na map cewa, an nuna wasu kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harsunan faransanci da Spaniyanci a babban baje kolin littafai na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Sandiago na kasar Chille, wanda ya kara kayatar da wannan baje koli da ake gabatarwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli yana da daga cikin irinsa masu matukar muhimmanci da ake gudanarwa a kasar, wanda kuma a cikinsa ana baje littafai da suka danganci akidu na addinai da al'ummomin da suka gabata a cikin kasashen duniya, musamman ma dadaddu daga cikinsu, wanda kuma addinin muslunci na daga ciki.

An nuna wasu kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harsunan faransanci da Spaniyanci a babban baje kolin littafai na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Sandiago na kasar Chille, wanda ya kara kayatar da wannan baje koli na kasar Chille.

782994




captcha