IQNA

An Bude Baje Kolin Littafan Musulunci Na Shekara-Shekara A Kasar Kuwait

13:23 - April 30, 2011
Lambar Labari: 2113999
Bangaren kasa da kasa, an baje kolin littafan addinin muslunci na shekara-shekra da aka saba gudanarwa a kasar Kuwait, tare da halartar cibiyoyin ilimi da masu buga littafai daga sassa daban-daban na duniya, musamman a kasashen musulmi da na larabawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin yanar gizo an habarta cewa, an baje kolin littafan addinin muslunci na shekara-shekra da aka saba gudanarwa a kasar Kuwait, tare da halartar cibiyoyin ilimi da masu buga littafai daga sassa daban-daban na duniya, musamman a kasashen musulmi da na larabawa, inda suka baje littafan da suka kawo wurin.

A bagare guda kuma an bayyana cewa an giirmama wani makarancin kur'ani mai tsarki na kasar Iraki da ya taka rawar gani a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Kuwait a matasayi na kasashen musulmi da na larabawa, inda ba shi kyautuka na girmamawa da nufin kara karfafa gwiwarsa da sauran makaranta.

Gasar karatun dai an gudanar da ita a bangarorin daban-daban, da hakan ya hada da matakai na farko, inda hakan ya fara daga juzu'I na farko zuwa na biya da kuma na goma har zuwa sha biyar, bayan na kuma an gudanar da bagare na krashe wanda ya kunshi dukkanin kur'ani mai tsarki daga farko har zuwa karshe.

Baje kolin littafan addinin muslunci na shekara-shekra da aka saba gudanarwa a kasar Kuwait, tare da halartar cibiyoyin ilimi da masu buga littafai daga sassa daban-daban na duniya, musamman a kasashen musulmi da na larabawa, na daga cikin muhimman baje kolin littfai na kasashen musulmi.

783047

captcha