IQNA

Yin Allawadai Da Zalunci Kan Al’ummar Bahrain Baai Wadatar Ba

19:46 - April 30, 2011
Lambar Labari: 2114723
Bangaren kasa da kasa, yin allawadai da zaluncin mahukuntan kasar Bahrain kawai ba zai taba taimakon al’ummar kasar ba, domin kuwa azzaluman mahukuntan gidan sarautar ali-khalifa tare sojojin mamayar Saudiyya a cikin kasar Bahrain suna ci gaba da yin kisan gilla akan fararen hula babu kyakyaftawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ya yi da daya daga cikin jagororin matasan kasar Bahrain Abdulrauf Shayib ya bayyana cewa, yin allawadai da zaluncin mahukuntan kasar Bahrain kawai ba zai taba taimakon al’ummar kasar ba, domin kuwa azzaluman mahukuntan gidan sarautar ali-khalifa tare sojojin mamayar Saudiyya a cikin kasar Bahrain suna ci gaba da yin kisan gilla akan fararen hula babu kyakyaftawa, da nufin mayar da rikicin zuwa na mazhaba.
Babban malamin addnin muslunci a kasar Bahrain Ayatollah Isa Ahmad Kasim ya bayyana cewa, rusa masallatai mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya suke yi a acikin kasar Bahrain babban cin zarafi ne da keta alfarmar addinin muslunci, shehin malamain ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar hudubar juma’a abirnin Manama.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain Nabil Rajab ya bayyana cewa, gidan sarautar kasar ta Bahrain na kokarin tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, da nufin kawar da hankulan al’ummomin duniya kan barnar da suke tafkawa a cikin kasar, suna yin hakan ne kuwa ta hanyar rusa masallatai da wuraren tarukan addini na mabiya mazhabar iyaln gidan manzon Allah masu rinjaye a kasar. 781812
captcha