IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zama A kasar Faransa Domin Kalubantar Kyamar Musulunci

13:53 - May 01, 2011
Lambar Labari: 2115231
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Faransa za su gudanar da wani zama na musamman domin kalubalantar akidar kyamar muslunci da kuma abubuwan da suke gani na danne hakkokinsu a kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar giz na atlainfo an bayyana cewa, babban daraktan cibiyar addnin muslunci da kuma babban masallacin birnin Lion na kasar Faransa Kamil Kabtan ya bayyana cewa, wannan masallacin da kowa da kowa ne, ba kamar yadda jami’an ma’aiktar tsaron kasar Amurka suka fada ba kan cewa wuri ne na taruwar ‘yan ta’adda da suke yin barazana ga nahiyar turai.
Bayanin ya ci gaba da cewa, dukkanin mabiya addinin muslunci suna hakki su zo su gudanar da lamurran ibada acikin masallaci daga ko’ina cikin duniya, kuma abin da jami’an na ma’aikatar tsaron kasar Amurka suka fada babu kamshin gaskiya a cikinsa, domin kuwa dukkanin mabiya addinin msulunci sun yi imani da zaman lafiya tsakaninsu da sauran mabiya addinai.
Babban daraktan cibiyar addnin muslunci da kuma babban masallacin birnin Lion na kasar Faransa Kamil Kabtan ya bayyana cewa, wannan masallacin da kowa da kowa ne, ba kamar yadda jami’an ma’aiktar tsaron kasar Amurka suka fada ba kan cewa wuri ne na taruwar ‘yan ta’adda.
783546

captcha