IQNA

Mabiya Addinin Kirista Na Samun Hakkokinsu A Iran Kamar Musulmin Kasar

20:27 - May 01, 2011
Lambar Labari: 2115419
Bangaren siyasa da zamantakewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Lebanon Malam Muhammadi a lokacin da yake kai wata ziyara wa jagoran kirista na kasar Lebanon Bushara Al-rai ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar ta Iran.
A bangare guda bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Auzbakistan ta gudanar da zama, domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci mabiya addinin muslunci na kasar, musamman ma matsalolin da suke fuskanta ta fuskacin karancin ilimi da sauransu.
Bayanin ya ci gab ada cewa kasar Auzbakistan wadda day ace daga cikin kasashen musulmi da ta shahara ta fuskacin tarihin addini da kuma rubuce-rubuce, wadanda ba a gushe ba har inda yau take ana yin amafani da sua a duniyar musulmi, amma a halin yanzu kasar tana fuskatar karancin makarntu, da hanyoyi na bunkasa ilimin addinin msulunci. 783319
captcha