Bangaren ilimi da nazari:An kawo karshen zagon bada horo kan usulin musulunci ga yara kanana da matasan Tataristan da aka gudanar a masallacin birnin Urrus na wannan kasa kuma an bas u wannan horo ne a cikin harshen larabci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; An kawo karshen zagon bada horo kan usulin musulunci ga yara kanana da matasan Tataristan da aka gudanar a masallacin birnin Urrus na wannan kasa kuma an bas u wannan horo ne a cikin harshen larabci.Wadanda suka halarci wannan zangon karatu da bada horo sun gamsu da yadda aka gudanar da kuma yanayin da malamai suka bayar da wannan darasi da horo ga yara kanana da matasa na kasar.
784511