IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Shiri Na Karatun Kur’ani Ta Hanyar Wayar Tarho A Kuwait

16:35 - May 04, 2011
Lambar Labari: 2117508
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shirin na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ta hanayar wayar tarho a kasar Kuwait, wanda cibiyar raya harkokin addinin muslunci da kuma yad akoyarwar kur’ani mai tsarki ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, wanda ya kebanci mata masu sha’awar koyon karatun kur’ani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Kuwait ta Al-ray an bayyana cewa, an fara gudanar da wani shirin na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ta hanayar wayar tarho a kasar Kuwait, wanda cibiyar raya harkokin addinin muslunci da kuma yad akoyarwar kur’ani mai tsarki ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, wanda ya kebanci mata masu sha’awar koyon karatun kur’ani mai tsarki a fadin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri ya samu gagarumar karbuwa daga mata a sassa daban-daban na kasar, kuma daga cikin abin da ya kunsa har da koyarwa da kuma yin gyara ga wadanda suka riga suka koya, domin sanin ka’idojin karatu da kuma yinsa daidai da tajwidinsa.
An fara gudanar da wani shirin na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ta hanayar wayar tarho a kasar Kuwait, wanda cibiyar raya harkokin addinin muslunci da kuma yad akoyarwar kur’ani mai tsarki ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, wanda ya kebanci mata masu sha’awar koyon karatun kur’ani.
785919

captcha