Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin mabiya addinin muslunci a kasar Faransa Muhammad Musavi ya bayyana cewa, addinin musulunci addini da ke girmama dukkanin ‘yan adam, kamar yadda yake kare hakkokinsu, duk kuwa da yadda wasu suke kokarin fassara wannan addini a matsayin addinin ta’addanci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CFCM an bayyana cewa, shugaban kwamitin mabiya addinin muslunci a kasar Faransa Muhammad Musavi ya bayyana cewa, addinin musulunci addini da ke girmama dukkanin ‘yan adam, kamar yadda yake kare hakkokinsu, duk kuwa da yadda wasu suke kokarin fassara wannan addini a matsayin addinin ta’addanci sakamakon rashin fahimta da jahilcinsa.
Musulmin kasar Faransa za su gudanar da zamansu na shekarashekara a cikin makonni biyu masu zuwa, domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci harkokin addinin muslunci da kuma yanayin rayuwarsu ta zamnatakewa a kasar da sauran batutuwa da suka shafe su musamman ma ta fuskacin yanci da walwalar addini.
A wani labari dabari da yanaklto daga shafin sadarwa na yanar gizo nalejdd an bayyana cewa, shugaban masallacin birnin paris fadar mulkin kasar Faransa Dalil Bubakar ya bukaci da a dage gudanar da zaben shugaban kwamitin musulmin kasar Faransa zuwa wani lokaci nan gaba, saboda rashin samun daidaito tsakanin musulmin yankunan kasar, da suke da hakkin zabar wanda suke ganin ya dace da rike wannan babbar amana.
Ya ci gaba da cewa wasu yankunan kasar faransa suna da musulmi da dama, wasu kuma akwai karancin musulmia acikinsu, saboda haka ya kamata har wadanda suke da karancin musulmin a basu damar shiga cikin wannan zabe, ta yadda hakkin wani ba zai saraya ba, wanda kuma hakan na bukatr karin lokaci kafin hada sunayen dukkanin musulmin yankuna.
785539