IQNA

Yahudawan sahyuniya Sun Kone Wani Masallaci Kurmus Yankunan Palastinawa

12:52 - May 05, 2011
Lambar Labari: 2117748
Bangaren kasa da kasa, wasu yahudawan sahyuniya yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi sun kai farmaki kan wasu yankunan palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kone wani masallaci mallakin palastinawa, kuma yanzu haka ma sun sha ba tare da an dauki matakan hukunta su ba.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na trouvetam an bayyana cewa, wasu yahudawan sahyuniya yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi sun kai farmaki kan wasu yankunan palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kone wani masallaci mallakin palastinawa, kuma yanzu haka ma sun sha ba tare da an dauki matakan hukunta su ba lamarin da ke tabbatar da cewa an shirya hakan ne tsakaninsu da mahukuntansu.

Da dama daga cikin palastinawa mazauna yankunan gabar yamma da kogin Jordan suna kokawa kan matsalolin da suke fuskanta na rashin tsaro, sakamakon yadda yahudawan 'yan kaka guida da suke dauke da makamai sukan kai farmaki kansu, wasu lokuta kuma hard a kashe su da kone kaddarorinsu.

Wasu yahudawan sahyuniya yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi sun kai farmaki kan wasu yankunan palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kone wani masallaci mallakin palastinawa, kuma yanzu haka ma sun sha ba tare da an dauki matakan hukunta su ba.

786528

captcha