Bangaren kasa da kasa, an sanar da sunayen mutanen da za su shiga gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, bayan da aka kawo karshen yin rijista ga masu sha'awar shiga wannan gasa a dukkanin bangarorn da za agudanar da ita.
Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, a wani labarii da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran wam an bayyana cewa, an sanar da sunayen mutanen da za su shiga gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, bayan da aka kawo karshen yin rijista ga masu sha'awar shiga wannan gasa a dukkanin bangarorn da za a gudanar da ita a cikin makonni masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa dai an fara gudanar da ita net un a cikin makon da ya gabata, kuma ta samu halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa, musamman kasashen yankin gabas ta tsakiya.
An kawo karshen wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da aka yi take da ayar tadabburin kur'ani da tunani a kan ayayinsa masu tsarki, wadda aka gudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwancin kasar hadaddiyar daular larabawa.
Yanzu haka dai an sanar da sunayen mutanen da za su shiga gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, bayan da aka kawo karshen yin rijista ga masu sha'awar shiga wannan gasa a dukkanin bangarorn da za agudanar da ita.
787359