IQNA

Musulmin Indiya Sun Halarci Bukin Tunawa Da Ranekun Shahadar Fatima

Bangaren siyasa da zamantakewa;Musulmin a kasar Indiya sun halarci da ci gaba da halartar tarukkan tunawa da kuma raya ranekun da Saida Fatima Zahra (AS) ta yi shahada da aka gudanar a Huseiniyoyi da masallatai na garuruwa da biranai daban daban na kasar ta Indiya.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Musulmin a kasar Indiya sun halarci da ci gaba da halartar tarukkan tunawa da kuma raya ranekun da Saida Fatima Zahra (AS) ta yi shahada da aka gudanar a Huseiniyoyi da masallatai na garuruwa da biranai daban daban na kasar ta Indiya.Said Hasan Razae mashahurin malami da kuma ya gabatar da jawabi a garin Jalalpur da ke lardin Utarparadesh a kasar ta Indiya a wani taron manema labarai ya bayyana cewa: abin farin ciki da kaanciyar hankali fda fara'a ne yadda aka gudanar da irin wadannan taruruka da kuma yadda mutane suka fito masu yawan gasket.


787306