Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron kasar Bahrain tare da sojojin mamayar Saudiyya sun fara kone gidajen masu neman sauyi a kasar, baya ga ci gaba da kame su da azabtar da su a gidajen kurkukun masarautar kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarata cewa, rahotanni sun habarta cewa a jiya jami'an tsaron kasar Bahrain tare da sojojin Saudiyya sun kai farmaki kan gidan Mahdi Ayyad, daya daga cikin jagororin masu neman sauyi a hakokin siyasar kasar dake yankin Barbar a kusan birnin Manama, inda suka kone gidan da dukkanin kaddarorin da ke ciki kurmus, tare da fitar da iyalansa da karfin tuwo daga gidan, da cin zarafinsu a bainar jama'a.
Yanzu haka dai wasu lauyoyi na kasa da kasa masu zaman kansu sun shigar da kara kan mahukuntan kasar Bahrain da na Saudiyya, kan kisan gillar da suke yi wa fararen hula a kasar ta Bahrain da ke neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa, kamar yadda wani babban lauya a kasar Masar shi ma ya shigar da kara kan sarakunan Bahrain da na saudiyya, kan rusa masallatai da kone kur'ani mai tsarki da suka yi a Bahrain, da sunan murkushe masu bore.
Jami'an tsaron kasar Bahrain tare da sojojin mamayar Saudiyya sun fara kone gidajen masu neman sauyi a kasar, baya ga ci gaba da kame su da azabtar da su a gidajen kurkukun masarautar kasar ta Bahrain.
787898