Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da gudanar da taron baje kolin littafai na kasashen duniya a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran, wanda ke samun halartar mancibiyoyin buga littafai na kasa da kasa, daga ciki kuwa har da manyan cibiyoyin buga littafai na kasar Lebanon.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa bangaren yada labaransa na birnin Tehran ya habarta cewa ana ci gaba da gudanar da taron baje kolin littafai na kasashen duniya a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran, wanda ke samun halartar mancibiyoyin buga littafai na kasa da kasa, daga ciki kuwa har da manyan cibiyoyin buga littafai na kasar Lebanon da suka kawo irin nasu littafan da suke bugawa.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da jagooran dakin cibiyar Dar al yasin daga kasar Syria ya bayyana cewa, sun kawo ababe da dama da suka danganci ayyuka na kur'ani mai tsarki, musamman ma wadanda suke da danganta da harkar rubutun kur'ani mai tsarki, da kuma wasu daga cikin littafai da suka danganci koyarwar addinin muslunci.
An nuna wani kur'ani da aka rubuta da wani shiri na musamman na na'ura mai kwakwalwa a baje kolin kasa da kasa na littafai da ake gudanarwa a birnin Tehran, wanda ke samun halartar cibiyoyin buga littafai na kasashen duniya.
Taron baje kolin littafai na kasashen duniya a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran, wanda ke samun halartar mancibiyoyin buga littafai na kasa da kasa.
787822