Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada mujallar cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci, wadda ke gudanar da ayyukanta na habbaka fahimta tsakanin dukkanin bangarorin musulmi da mazhabobinsu, ta yadda hakan zai bayar da damar magance matsalolin da ke fuskantar al’ummar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sociorel cewa an buga tare da yada mujallar cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci, wadda ke gudanar da ayyukanta na habbaka fahimta tsakanin dukkanin bangarorin musulmi da mazhabobinsu, ta yadda hakan zai bayar da damar magance matsalolin da ke fuskantar al’ummar musulmi musamman ma a wannan lokaci.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
Gudanar da sallar juma’a abirnin Rom fadar mulkin kasar Italia a babban dandalin da ke tsakiyar birnin, domin nuna rashin amincewa da matakin da mahukuntan suka dauka na kin bayar da izinin gina masallaci a birnin, na tattare da babban sako.
788373