Bangaren siyasa da zamantakewa; a cikin shekaru uku na baya bayan nan sabanin shekarun da suka gabata an samu Karin yawan masallatai a kasar Ukrain da kashi hamsin cikin dari.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; a cikin shekaru uku na baya bayan nan sabanin shekarun da suka gabata an samu Karin yawan masallatai a kasar Ukrain da kashi hamsin cikin dari.An nakalto daga shafin Internet na Islam Ru da kuma jaridar Kommentarii da ke fitowa a kowa ne mako a kasar Ukrain sun kawo da labarin karuwar yawan gine gine na masallatai a kasar ta Ukrain musamman a lardin Kherson na kasar ta Ukrain.
789320