IQNA

An Cire Rigar Kariya Daga Wuyan Dan Majalisar Dokokin Faransa Mai Gaba Da Musulunci

15:57 - May 12, 2011
Lambar Labari: 2121038
Bangaren kasa da kasa, an cire rigar kariya daga wuyan dan majalisar dokoin kasar faransa mai tsananin gab ada addinin Musulunci, bisa samunsa da laifin tunzura jama'a wajen nuna kiyayya da addinin muslunci da kuma mabiya awannan addini a cikin kasar faransa.


Kamfanin dillancin labaran iqna iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo naleparisien an bayyana cewa, an cire rigar kariya daga wuyan dan majalisar dokoin kasar faransa mai tsananin gab ada addinin Musulunci, bisa samunsa da laifin tunzura jama'a wajen nuna kiyayya da addinin muslunci da kuma mabiya awannan addini a cikin kasar faransa baki daya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama da masu yaki da kyamar addinai da marassa rinjaye na kasar faransa da ma wasu daga cikin kasashen nahiyar turai, gami da kungiyoyin musulmin kasar ne suka shigar da kara kan mutumin, bisa la'akari da cewa abin da yake ya sabawa dukkanin dokokin kasar.

An cire rigar kariya daga wuyan dan majalisar dokoin kasar faransa mai tsananin gab ada addinin Musulunci, bisa samunsa da laifin tunzura jama'a wajen nuna kiyayya da addinin muslunci da kuma mabiya awannan addini a cikin kasar faransa.

789872



captcha