Bangaren kasa da kasa; a yau ashirin da biyar ga weatan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in shekara ta hijira shamsiya a daidai wannan rana ta zagayewar mamaye Palasdinu da haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi za a gudanar da wani gagaramin taron nuna goyan bayan al'ummar Palsdinu a gaban ofishin jakadancin Palsdinu da ke birnin Jidda na kasar Saudiya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a yau ashirin da biyar ga weatan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in shekara ta hijira shamsiya a daidai wannan rana ta zagayewar mamaye Palasdinu da haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi za a gudanar da wani gagaramin taron nuna goyan bayan al'ummar Palsdinu a gaban ofishin jakadancin Palsdinu da ke birnin Jidda na kasar Saudiya. Irin wannan taron nuna goyan baya ga al'ummar ta palsdinu da aka mamaye ana gudanar da shi a kasashe daban daban na muslmi da na larabawa inda al'ummomin kasashen musulmi da wadanda ba musulmi ba masu hankorin kiyayye hakkin bil adama da kuma yakar zalunci ke nuna goyan bayansu ga al'ummar Palasdinu.
791152