IQNA

An Buga Tare Da Yada Littafin Ibrahim Bn Al’ajdabi Na Rayuwa Da Kufafenta

19:36 - May 15, 2011
Lambar Labari: 2122635
Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada littafin rayuwa da kufafenta na Ibrahim Ajdabi wanda cibiyar yada al’adun muslunci ta dauki nauyin bugawa tare da hadin hadin gwiwa da babbar cibiyar yada al’adu ta ISESCO.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an buga tare da yada littafin rayuwa da kufafenta na Ibrahim Ajdabi wanda cibiyar yada al’adun muslunci ta dauki nauyin bugawa tare da hadin hadin gwiwa da babbar cibiyar yada al’adu ta ISESCO, da ke taka gagarumar ta fuskacin harkokin musulunci a kasashen musulmi.
A wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na le-coran an bayyana cewa, an saka tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin shafin yanar gizo a cikin harshen farasanci, tare da karatun kur’ani mai tsarki daga fitattun makaranta na duniyar musulmi, da nufin kara fadada ayyukan kur’ani a shafukan yanar gizo da ake ziyarta koina cikin duniya.
Bugu da kari kan tarjamar kur’ani mai tsarki a acikin harshen faranci dake cikin wannan shafi na yanar gizo, za a iya sanin wasu abubuwan da suka shafi kur’ani, kamar sanin adadin ayoyin da ke cikin sura, ko kuma dalilan safkar ayoyi da kuma tafsirin ma’nar wasu kalmomin kur’ani, da suke bukar bayani ta yadda mai karatu ba zai sha wahala wajen gane ma’narsu ba.
791102

captcha