IQNA

An Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Goyan Bayan Al'ummar Bahrain A Turkiya

17:14 - May 16, 2011
Lambar Labari: 2123301
Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin da hudu ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne aka gudanar da wata gagaramar zanga-zangar nuna goyan baya ga al'ummar kasar Bahrain da ake nunawa zalunci da danniya ta hanyar yi masu kisan mummuke da kisan kiyashi kawai don sun fito suna nuna bukatar kawo canji da sauyi a siyasa da zamantakewar kasar kuma wannan zanga-zanga an gudanar da ita ne a birnin Istanbul na kasar ta Turkiya.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da hudu ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne aka gudanar da wata gagaramar zanga-zangar nuna goyan baya ga al'ummar kasar Bahrain da ake nunawa zalunci da danniya ta hanyar yi masu kisan mummuke da kisan kiyashi kawai don sun fito suna nuna bukatar kawo canji da sauyi a siyasa da zamantakewar kasar kuma wannan zanga-zanga an gudanar da ita ne a birnin Istanbul na kasar ta Turkiya.Dubban yan kasar Turkiya a wannan birni na Istambul ne suka fito fili a wanin jerin gwano suna sun agoyan bayansu ga al'ummar Bahrian a bangare daya suna yi allah wadai da tofin Allah tsine kan gwamnatin Bahrain da ke yiwa al'ummarta kisan kiyashi a wani al'amari mai daurin kai da kuma ban mamaki a fili karara tare da kiran kasashen duniya da hukumomi na ciki da na kasa da kasa da su yi wani hambasa domin kawo karshen wannan zalunci da ake nunawa al'ummar Bahrain.

791995

captcha