Bangaren siyasa da zamantakewa, daya daga cikin mambobin majalisar dokokin jamhuriyar muslunci ta Iran ya yi kira ga sauran takwarorinsa na majalisar da su taka gaggarumar rawa a abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya, bisa la'akari da yadda ake zaluntar mutane a wasu kasashen tare da hukumomi da hadin baki da kashen yammacin turai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, daya daga cikin mambobin majalisar dokokin jamhuriyar muslunci ta Iran ya yi kira ga sauran takwarorinsa na majalisar da su taka gaggarumar rawa a abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya, bisa la'akari da yadda ake zaluntar mutane a wasu kasashen tare da hukumomi da hadin baki da kashen yammacin turai.
A wani labarin kuma, daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ya bayyana cewa za abude wata bababr cibiyar kula da bincike da nazari kan tarihin manzon Allah (SAW) a birnin Jidda na kasar, domin bayar da dama ga masu bincike su kara fadada ayyukansu ta wannan fuska, musamman bisa la'akari da muhimmancin da ke tattare da hakan.
Wasu bayanan sun tabbatar da cewa, tun bayan da ma'aikatar kula da ayyukan addinin ta kasar saudiyya ta bayyana hakan, da dama daga cikin masana da manazarta sun bayyana cewa hakan zai taimaka musu matuka, matukar dai za a samar da littafai na sahihin tarihi wanda ba agurbata ba, ko saka ra'ayi na bangaranci da nufin tallata wata akida.
792533