Bangaren kasa da kasa, an bude wata babbar cibiyar kula da ayyukan nazari da bincike kan kur'ani mai tsarki da kuma ilmominsa a yankin Aakaba na kasar Jordan, inda za a rika gudanar da harkokin bincike da suka danganci kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sabil an bayyana cewa, an bude wata babbar cibiyar kula da ayyukan nazari da bincike kan kur'ani mai tsarki da kuma ilmominsa a yankin Aakaba na kasar Jordan, inda za a rika gudanar da harkokin bincike da suka danganci kur'ani mai tsarki a kasar da ma yankin baki daya.
Babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ya bayyana cewa za abude wata bababr cibiyar kula da bincike da nazari kan tarihin manzon Allah (SAW) a birnin Jidda na kasar, domin bayar da dama ga masu bincike su kara fadada ayyukansu ta wannan fuska, musamman bisa la'akari da muhimmancin da ke tattare da wannan aiki.
Wasu bayanan sun tabbatar da cewa, tun bayan da ma'aikatar kula da ayyukan addinin ta kasar saudiyya ta bayyana hakan, da dama daga cikin masana da manazarta sun bayyana cewa hakan zai taimaka musu matuka, matukar dai za a samar da littafai na sahihin tarihi wanda ba agurbata ba, ko saka ra'ayi na bangaranci da nufin tallata wata akida wadda ba hada dukkanin musulmi ba.
792467