Bangaren kasa da kasa; kungiyar hadin kan kasashen musulmi a cikin wani bayani da ta fitar a dangane da zagayowar shekaru sattin da uku da mamaye Palsdinu da kafa gwamnatin yaudara ta Isra'ila a yankin ta bayyana cewa kasashe da daman a duniya da j=hukumomi da mu'asisoshi na duniya na bukatar kafa gwamnatin palsdinu mai cin gashin kanta da yanci.