IQNA

Barazil Ta Bukaci Ta Zama Mamba Mai Sa Ido A Kungiyar Kasashen Musulmi

13:00 - May 18, 2011
Lambar Labari: 2124494
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Brazil ta bukaci ta zama mamba mai sanya ido a cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya OIC da nufin kara samun kusantar juna tsaknainta d sauran kasashen musulmi baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalato daga shafin yanar gizo na jaridar Al-bayan ta hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa, gwamnatin kasar Brazil ta bukaci ta zama mamba mai sanya ido a cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya OIC da nufin kara samun kusantar juna tsaknainta d sauran kasashen musulmi baki daya, lamarin da ake ganin zai samu karbuwa daga kungiyar.
Bayanin ya ci gaba da cewa jakadan kasar Brazil a kasar Saudiyya ne ya mika wannan takarda da take dauke da wannan bukata ta kasarsa ga babban sakataren kungiyar Ihsan Auglu a babban ofishin kungiyar da ke birnin Jidda, inda ya sheda masa irin bukatar da kasarsa take da ita wajen ganin ta zama mamba mai sa ido a wannan babbar kungiya. A nasa bangaren babban sakataren kungiyar ya ce za su duba su ga abin yi kan hakan.
Gwamnatin kasar Brazil ta bukaci ta zama mamba mai sanya ido a cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya OIC da nufin kara samun kusantar juna tsaknainta d sauran kasashen musulmi baki daya da suke mambobi a wannan kungiya.
793305

captcha