IQNA

Kungiyar OIC Ta Yi Allawadai Da Kai Hari Kan Fararen Hula Palastinawa

12:58 - May 18, 2011
Lambar Labari: 2124501
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka da yin Allawadai kan kai harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a kan palastinawa farren hula, da suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu da kafa kasar yahudawa da aka yi a cikin kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka da yin Allawadai kan kai harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a kan palastinawa farren hula, da suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu da kafa kasar yahudawa da aka yi a cikin kasarsu tare da hadin gwiwa tsaknainyahudawan da kasashen yammacin turai.
A wani rahoton kuma an bayyana cewa a wani labari da aka nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na middle East Monitor cewa, ana shirin bude hanyoyin karkashin kasa da yahudawan sahyuniya suka gina karkashin masallacin Qods mai alfarma, a lokacin da al’ummomin duniya gami da shugabannin larabawa suka yi gum da bakinsu kan wannan tabargaza ta yahudawan sahyuniya a wurare masu tsarki na al’ummar musulmi.
Tun bayan da yahudawan sahyuniya suka fara gudanr da wannan aiki, masu ‘yancin siyasa daga cikin kasashen musulmi da kuma ‘yan kadan daga cikin kasashen larabawa, sun nuna rashin amincewarsu da wannan mummanan aiki da ke samun cikakken goyon baya daga gwamnatocin Amurka da munafukan larabawa, musamman ma wadanda suke da dangantaka ta zahiri da haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma masu dangantaka ta boye.
793228


captcha