Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Azarbaijan ya yi kira da a kawo karshen kyamar addinin Musulunci a cikin kasashen da gabaci da yammaci, ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manyan malan addinin Musulunci na kasar a wani zama da ya gudanar tare da su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo an bayyana cewa, shugaban kasar Azarbaijan ya yi kira da a kawo karshen kyamar addinin Musulunci a cikin kasashen da gabaci da yammaci, ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manyan malan addinin Musulunci na kasar a wani zama da ya gudanar tare da su a birnin Bako fadar mulkin kasar.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan yadda mata musulmi suke shiga cikin harkokin siyasa da zamantakewa a wasu kasashen nahiyar turai, musamman a kasashen Birtaniya da kuma da Faransa inda ked a mabiya addinin Musulunci da dama.
Bayanin ya ci gaba da cewa mata mabiya addinin muslunci a kasashen Faransa da kuma Birtaniya suna taka gagarumar a cikin harkoki da dama musamman na zamantakewa, a kan haka ne sukan gudanar da zama a kowace sheka a birnin Paris na kasar faransa domin yin bita kan irin ci gaban da suka samu ta wannan fuska a cikin shekara.
794106