IQNA

Jami'ar Azhar Ta Amince Da Kara Yawan Kasafin Kudin Gasar Kur'ani A Kasar

19:40 - May 21, 2011
Lambar Labari: 2125944
Bangaren kasa da kasa, jamia'r Azhar ta kasar Masar ta amince da kara yawan kasafin kudaden da ake kashewa bangaren gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a fadin kasar, wanda bangaren kula da ayyukan kur'ani mai tsarki na jami'ar ke daukar nauyin sa ido.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Akhbar ta kasar an bayyana cewa, jamia'r Azhar ta kasar Masar ta amince da kara yawan kasafin kudaden da ake kashewa bangaren gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a fadin kasar, wanda bangaren kula da ayyukan kur'ani mai tsarki na jami'ar ke daukar nauyin sa ido da ma gudanar da su.

A wani labari da ya nakalto daga shafin yanar giz na atlainfo an bayyana cewa, babban daraktan cibiyar addnin muslunci da kuma babban masallacin birnin Lion na kasar Faransa Kamil Kabtan ya bayyana cewa, wannan masallacin da kowa da kowa ne, ba kamar yadda jami’an ma’aiktar tsaron kasar Amurka suka fada ba kan cewa wuri ne na taruwar ‘yan ta’adda da suke yin barazana ga nahiyar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, dukkanin mabiya addinin muslunci suna hakki su zo su gudanar da lamurran ibada acikin masallaci daga ko’ina cikin duniya, kuma abin da jami’an na ma’aikatar tsaron kasar Amurka suka fada babu kamshin gaskiya a cikinsa, domin kuwa dukkanin mabiya addinin msulunci sun yi imani da zaman lafiya tsakaninsu da sauran mabiya addinai daban-daban.

795062



captcha