IQNA

Limaman Masallatai A Birnin Strasburg Za Su Gudanar Da Wani Zama

19:39 - May 21, 2011
Lambar Labari: 2125947
Bangaren kasa da kasa, limaman masallatai a yankin Strasburg na kasar faransa za su fara gudanar da wani zamansu na shekara-shekara domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin addini da sauran lamurran mabiya addinan addinin muslunci.

Kamfanin dillancin larabaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, limaman masallatai a yankin Strasburg na kasar faransa za su fara gudanar da wani zamansu na shekara-shekara domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin addini da sauran lamurran mabiya addinan addinin muslunci a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, dukkanin mabiya addinin muslunci suna hakki su zo su gudanar da lamurran ibada acikin masallaci daga ko’ina cikin duniya, kuma abin da jami’an na ma’aikatar tsaron kasar Amurka suka fada babu kamshin gaskiya a cikinsa, domin kuwa dukkanin mabiya addinin msulunci sun yi imani da zaman lafiya tsakaninsu da sauran mabiya addinai.
Babban daraktan cibiyar addnin muslunci da kuma babban masallacin birnin Lion na kasar Faransa Kamil Kabtan ya bayyana cewa, wannan masallacin da kowa da kowa ne, ba kamar yadda jami’an ma’aiktar tsaron kasar Amurka suka fada ba kan cewa wuri ne na taruwar ‘yan ta’adda.
795018

captcha