Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa wahoton cewa; a ranar ashirin da shida ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa za a gudanar da wani taro da zai yi nazari da bincike kan lamari da salon siyasa a cikin addinin musulunci.Mahalarta wannan taro na birnin Paris fadar mulkin kasar ta Faransa za su yi dogon nazari da bincike kan siyasa a cikin tsarin addinin musulunci domin daukan darasi da kuma tunanin irin hanyoyin day a kamata su bi da yin aiki da hakan zai taimaka masu warware matsalolin da suke fuskanta a siyasarsu ta yau.
795427