Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da tarukan makon addinin muslunci a Roka na kasar Italia, wanda kungiyar kula da ayyukan al'adu da bunkasa ilimin addinin muslunci ta duniya ISESCO ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan mako.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an bayyana cewa, an fara gudanar da tarukan makon addinin muslunci a Roka na kasar Italia, wanda kungiyar kula da ayyukan al'adu da bunkasa ilimin addinin muslunci ta duniya ISESCO ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan mako da muke ciki.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta fitar da wani da a cikinsa take bayyana cewa, samun fahimtar juna tsakanin kungiyoyin hamas da Fatah, wani sakamako ne daga cikin nasarar juyin da aka samu a kasar Masar, wanda ke tabbatar da cewa fuskar siyasar kasar ta kawo rarraba tsakanin al'umma ta fara kawo karshe, wanda aka ga haka a tsawon lokacin tsohuwar gwamnatin kama karya ta kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa ya zama wajibi ga dukkanin bangarorin palastinawa da su taka gagarumar rawa wajen ganin cewa an dunke duk wata baraka da aka samu a tsakaninsu sakamakon siyasar wasu gwamnatocin yankin, wadanda bas u son ganin alkhairi a cikin al'ummar larabawa da na musulmi, domin kare manufarsu ta kawance da yahudawa da Amurkawa.
797534