Bangaren kasa da kasa: A birnin Alonn na kasar Faransa a ranar takwas ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar da wani taron bincike da nazarin matsalolin da musulmi ke fuskanta a baya bayan nan a kasar ta Faransa da kuma sauran lamura sabbi na musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoon cewa: A birnin Alonn na kasar Faransa a ranar takwas ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar da wani taron bincike da nazarin matsalolin da musulmi ke fuskanta a baya bayan nan a kasar ta Faransa da kuma sauran lamura sabbi na musulmi. Manazarta da masu bincike da kuma malaman addini za su kasance guri guda domin yin nazari da bincike kan yadda za a magance irin matsaloli a yan kwanani da shekarun nbaya bayan nan da musulmi a kasar Faransa ke fuskanta da kuma sabbin lamurra da suka shafi musulmi tare da yin la'akari da dalilin da suka jawo irin wadannan matsaloli da hanyar magance su.
797639