Bangaren kasa da kasa, za a gina wata makaranta ta yara ‘yan mata musulmi a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda sheikh Thani Bin Abdullah na kasar Qatar zai dauki nauyin ginawa tare da hadin gwiwa da cibiyar bunkasa ayyukan al’adu da ilimin musulunci ta kasar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lahaonline an bayyana cewa, za a gina wata makaranta ta yara ‘yan mata musulmi a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda sheikh Thani Bin Abdullah na kasar Qatar zai dauki nauyin ginawa tare da hadin gwiwa da cibiyar bunkasa ayyukan al’adu da ilimin musulunci ta kasar.
Bayanin ya ci da cewa dag acikin muhimman ayyuakn da wannan makaranta za ta aiwatar bayan kammala gininta shi ne, koyar da yara ‘yan mata musulmi na kasar Birtaniya muhimman darussa na addini wadanda ba a koyar da su a makarantun gwamnati, bugu da kari kan hakan za akoyar da su wasu darussan na ilmin zamani, domin samun damar gudanar da harkokinsu na karatu.
Gina wata makaranta ta yara ‘yan mata musulmi a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda sheikh Thani Bin Abdullah na kasar Qatar zai dauki nauyin ginawa tare da hadin gwiwa da cibiyar bunkasa ayyukan al’adu da ilimin musulunci ta kasar Birtaniya na da matukar muhimmanci.
799125