IQNA

Musulmin kasar Masar Za Su Gyara Wata Majami’a Ta Kibtawa A Kasar Masar

16:48 - May 28, 2011
Lambar Labari: 2129703
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masu fasaha musulmi na kasar Masar za su gudanar da ayyukan gyara a babbar majami’ar nan ta kasar Masar da ke birnin Alkahira, bayan da wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayi wahabiyanci suka kai hari kanta a cikin makonnin da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, wasu daga cikin masu fasaha musulmi na kasar Masar za su gudanar da ayyukan gyara a babbar majami’ar nan ta kasar Masar da ke birnin Alkahira, bayan da wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayi wahabiyanci suka kai hari kanta a cikin makonnin da suka gabata sakamakon tunzura su da malaman wahabiyawan saudiyya ke yi.
Tun bayan da masu ra’ayin wahabiyancin da suke samun goyon baya daga gwamnatin Saudiyya suka kai farmaki a kan majami’oin mabiya addinin kiristanci a kasar Masar musamman a biranan Iskandariyya da Kahira, hakan ke ci gaba da fuskantar Allawadai daga al’ummomin kasar ta Masar da sauran musulmin duniya, inda ake bayyana hakan da cewa yunkuri ne Saudiyya ke na yamutsa lamurra a kasar Masar.
Yanzu haka dai wasu daga cikin masu fasaha musulmi na kasar Masar za su gudanar da ayyukan gyara a babbar majami’ar nan ta kasar Masar da ke birnin Alkahira, bayan da wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayi wahabiyanci suka kai hari kanta a cikin makonnin da suka gabata a kasar.
799122

captcha