Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a a lardin Tagsas na Amerika komitin dangantaka da kusanci tsakanin Amerikawa da musulunci ya gayyaci musulmi a wannan lardi da su halarci sallar rokon rowan sama. Komitin ya bukaci sauran mabiya addinai daban daban day a gudanar da irin wannan sallar ta rokon rowan sama domin an samu waraka daga matsalar karamcin rowan sama da jahar ta Tagsas a Amerika ke fuskanta.Wasu shafukan musulunci da kungiyoyi da cibiyoyi na Faransa sun yi nuni da wannan sako na magajin garin Tagxas a Amerika da fatar ganin firaministan Faransa ma ya yi ko yi domin gudanar da sallar rokon ruwa a Faransa ga sauran mabiya addinai domin magance matsalar rowan sama da iska .
799059