IQNA

An Yi Bahasi Kan Wani Littafi Mai Suna Sira Da Makomar Imam Musa Sadr

18:17 - May 28, 2011
Lambar Labari: 2129731
Bangaren kasa da kasa, an yi bitar wani littafi da aka rubuta kan tarihi da kuma gagarumar gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar kan harkokin addini da fadakarwa, da kuma makomarsa bayan sace da mahukuntan kasar Libya karkashin jagorancin Mu’ammar Gaddafi suka yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an yi bitar wani littafi da aka rubuta kan tarihi da kuma gagarumar gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar kan harkokin addini da fadakarwa, da kuma makomarsa bayan sace da mahukuntan kasar Libya karkashin jagorancin Mu’ammar Gaddafi suka yi a cikin shekaru sama da talatin da suka gabata a cikin kasar ta Libya bayan gayyatarsa da Gaddafin ya yi a hukumance.
Imam Musa Sadr dai shi ne wanda ya kafa gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon, wadda ta kai ga korar haramtacciyar kasar Isra’ila daga yankunan al’ummar Lebanon da ta mamaye, yanzu haka kuma masu gwagwarmaya suna yin koyi da shi wajen tsaya kan dugaduginsu wajen yakar haramtacciyar gwamnatin yahudawan da ke hankoron mamaye musu kasa.
An yi bitar wani littafi da aka rubuta kan tarihi da kuma gagarumar gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar kan harkokin addini da fadakarwa, da kuma makomarsa bayan sace da mahukuntan kasar Libya karkashin jagorancin Mu’ammar Gaddafi suka yi a kasar.
799087
captcha