IQNA

An Gudanar Da Zaman Kungiyar ISESCO Da Kuma Kungiyar Larabawan Faransa

13:47 - May 29, 2011
Lambar Labari: 2130199
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na kungiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta kasashen muslumi da kuma kungiyar larabawa mazauna kasar Faransa, da nufin samar da hanyoyin bunkasa ayyukan da suke gudanarwa na bai daya a kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na kungiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta kasashen muslumi da kuma kungiyar larabawa mazauna kasar Faransa, da nufin samar da hanyoyin bunkasa ayyukan da suke gudanarwa na bai daya a kasar da ma wasu daga cikin kasashen yammacin turai.

Babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ya bayyana cewa za abude wata bababr cibiyar kula da bincike da nazari kan tarihin manzon Allah (SAW) a birnin Jidda na kasar, domin bayar da dama ga masu bincike su kara fadada ayyukansu ta wannan fuska, musamman bisa la'akari da muhimmancin da ke tattare da hakan.

Wasu bayanan sun tabbatar da cewa, tun bayan da ma'aikatar kula da ayyukan addinin ta kasar saudiyya ta bayyana hakan, da dama daga cikin masana da manazarta sun bayyana cewa hakan zai taimaka musu matuka, matukar dai za a samar da littafai na sahihin tarihi wanda ba agurbata ba, ko saka ra'ayi na bangaranci da nufin tallata wata akida.

799603



captcha