Bangaren siyasa da zamantakewa; a yankin tsakiyar Asiya za agina masallaci mafi girma a yankin kuma za a gina shi ne a garin Almati na kasar Kazakistan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a yankin tsakiyar Asiya za agina masallaci mafi girma a yankin kuma za a gina shi ne a garin Almati na kasar Kazakistan.Gwamnatin wannan kasar ta kazakistan ce ta dauki dawainiya da nauyin gudanar da wannan aiki na gina masallaci mafi girma a yankin tsakiyar Asiya inda musulmi za su rika gudanar da dawainiyar ibadodinsu cikin kwanciyar hankali da kuma cikin nucuwa.
799160