IQNA

Musulmin Bangladesh Sun Karbi Abincin Halal Na Tailand

Bangaren siyasa da zamantakewa; musulmin Bangladesh a daidai wannan lokaci na kuratowar watan azumin Ramadana na shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da biyu hijira kamariya sun karbi abubuwan cid a sha na halaliya na Tailand da hannu bi biyu da aka shigar da su da nufin musulmin wannan kasa su yi amfani da su.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; musulmin Bangladesh a daidai wannan lokaci na kuratowar watan azumin Ramadana na shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da biyu hijira kamariya sun karbi abubuwan cid a sha na halaliya na Tailand da hannu bi biyu da aka shigar da su da nufin musulmin wannan kasa su yi amfani da su. Abin tuni a nan shugaban cibiyar kasuwanci ta kasar Bangladesh da kuma ke kula da shigowar kayayyakin kasashen ketare a cikin kasar ya bayyana cewa; ganin yadda abubuwan halaliya na Tailand suka samu karbuwa a wannan kasa a watan azumin Ramadana za a shigar da kayan Tailand da ake zaton za su kai biliyan takwas na Tuman.


799184