Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taro kan zakka da tsarkake dukiya a cikin addinin muslunci, wanda cibiyar bunkasa bincike kan al’adu da ilmomin addini a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda zai samu halartar masana da malaman addinin musulunci na kasar da ma wasu kasashen yammacin turai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo IIDR cewa, za a gudanar da zaman taro kan zakka da tsarkake dukiya a cikin addinin muslunci, wanda cibiyar bunkasa bincike kan al’adu da ilmomin addini a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda zai samu halartar masana da malaman addinin musulunci na kasar da ma wasu kasashen yammacin turai, musamman ma a kasar ta Birtaniya.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
Gudanar da sallar juma’a abirnin Rom fadar mulkin kasar Italia a babban dandalin da ke tsakiyar birnin, domin nuna rashin amincewa da matakin da mahukuntan suka dauka na kin bayar da izinin gina masallaci a birnin, na tattare da babban sako. 800236