IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taro Mai Taken ranar Kur’ani A Kasar Senegal

19:59 - May 30, 2011
Lambar Labari: 2131130
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zama mai taken ranar kur’ani a birnin Luka na kasar Senegal da zai yi dubi kan matsayin kur’ani da gudunmawarsa ga rayuwar dan adam, taron da zai samu halartar masana da malamai, gami da jami’an gwamnati da kuma wakilan kungiyoyin addini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na APS an bayyana cewa, za a gudanar da wani zama mai taken ranar kur’ani a birnin Luka na kasar Senegal da zai yi dubi kan matsayin kur’ani da gudunmawarsa ga rayuwar dan adam, taron da zai samu halartar masana da malamai, gami da jami’an gwamnati da kuma wakilan kungiyoyin addini daban-daban na kasar.
Kasar Senegal dai tana daya daga cikin kasashen musulmi na duniya da suke taka gagarumar rawa a bangarori da dama na yada ilmomin kur’ani a acikin kasashen kasashen musulmi musamman na nahiyar Afirka, lamarin da ke samun gagarumar karbuwa daga sauran al’ummomin musulmi, tae da jinjina wa kasar kan wannan namijin kokari da take yi.
Za a gudanar da wani zama mai taken ranar kur’ani a birnin Luka na kasar Senegal da zai yi dubi kan matsayin kur’ani da gudunmawarsa ga rayuwar dan adam, taron da zai samu halartar masana da malamai, gami da jami’an gwamnati da kuma wakilan kungiyoyin addinin musulunci.
800120

captcha